logo

HAUSA

Xi ya halarci zama na biyu na taron shekara shekara na majalisar NPC

2024-03-08 14:12:34 CMG Hausa

Majalisar wakilan jama'ar kasar Sin ta 14, ta gudanar da zama na 2 a yau Juma’a 8 ga watan Maris, taron da ya samu halartar shugaban kasar Xi Jinping, da sauran jagororin kasar ta Sin.

Shugaban zaunannen kwamitin majalisar Zhao Leji ya gabatar da rahoton aikin kwamitin, inda ya bayyana cewa, a bara, kwamitinsa ya aiwatar da ayyukan zartar da dokokin kasa da aka dora masa da karfafa bangarorin da suka shafi muhimman dokoki da bangarori masu tasowa da wadanda suka shafi kasashen wajen tare da kara kyautata tsarin shari’a da ke bukatar gyara na gaggawa wadanda ke da muhimmanci wajen biyan bukatun kyautata rayuwar jama’a da kuma kare tsaron kasa. Rahoton ya kuma bayyana cewa, a bara, kwamitin ya tattauna kan kudurorin doka 34 tare da zartar da 21 daga cikinsu. Ya ce yanzu haka, akwai dokoki 300 dake aiki a kasar Sin.

A yayin taron kuma, shugaban kotun koli ta al’umma ko SPC Zhang Jun ya gabatar da rahoton aiki, inda ya ce kasar Sin na mayar da hankali matuka ga kare hakkokin mallaka, na kamfanoni masu zaman kansu, da masu gudanar da sana’o’i, kuma tuni kotuna suka yi bita, da gyara wasu hukunce-hukunce 42 da aka yi bisa kuskure, wadanda suka shafi mutane 86 a shekarar 2023. 

Kaza lika, a cewar rahoton na SPC, kasar Sin ta himmatu wajen yaki da cin hanci, inda a shekarar ta bara, kotuna suka kammala shari’un cin hanci 24,000, da sauran wasu shari’un masu alaka da karya ka’idojin ayyukan hukuma, adadin matakan shari’ar da ya karu da kaso 19.9 bisa dari a shekara guda. (Saminu Alhassan)