MDD ta bayyana bukatar gaggauta zuba jari wajen karfafa tallafa wa mata a fannin tattalin arziki
2024-03-08 21:06:28 CMG Hausa
Hukumar kula da mata ta Majalisar Dinkin Duniya a jiya Alhamis ta fitar da wata tunatarwa mai karfi cewa zuba jari ga sha’anin mata na da matukar muhimmanci wajen habaka ci gaban tattalin arziki da samar da daidaton al’umma.
“Taken taron na bana wato zuba jari ga sha’anin mata yana tunatar da mu cewa kawo karshen kaskantar da mata na bukatar kudi”, a cewar Sakatare Janar na MDD Antonio Guterres a cikin wani sakonsa a jajibirin ranar mata ta duniya, yana mai jaddada bukatar gaggauta samar da hanyoyin kudi don tallafawa mata da ‘yan mata.
Hukumar ta yi kiyasin cewa ana bukatar karin dala biliyan 360 a kowace shekara ga kasashe masu tasowa don cike gibin da ke tsakanin jinsi a karkashin shirin ci gaba mai dorewa.
"Wannan duka ya dogara ne kan bude hanyoyin samar da kudade don samun ci gaba mai dorewa," a cewar Guterres, yana mai bayyana muhimmiyar rawar da kudade ke takawa wajen kawo karshen cin zarafin mata da inganta damawa da su a sassa daban-daban. (Yahaya)