logo

HAUSA

Sakatare Janar na MDD ya yi kira da tsagaita bude wuta a Sudan domin watan Ramadan

2024-03-08 13:56:46 CMG Hausa

Sakatare Janar na MDD Antonio Guterres ya yi kira da a tsagaita bude wuta a Sudan yayin watan Ramadan, yana mai cewa, dole ne a daukaka darajar watan.

Ya ce a wata mai zuwa za a cika shekara 1 da barkewar rikici tsakanin dakarun Sudan da na RSF. Yana mai cewa, rikicin ya tagayyara al’ummar Sudan, da kawo tsaiko ga hadin kan kasar. Ya yi gargadin akwai yiwuwar rikicin ya haifar da yaduwar rashin kwanciyar hankali mai tsanani a yankin, daga yankin Sahel zuwa yankin Kahon Afrika da kuma Bahar Maliya.

Ya ce yanzu lokaci ne na ajiye makamai domin yanayin jin kai a Sudan ya kai wani mummunan matsayi. (Fa’iza Mustapha)