logo

HAUSA

An yi zaman shugabannin rundunan sojojin kasashe mambobin kungiyar kasashen yankin Sahel

2024-03-08 20:33:27 CMG Hausa

Bayan wani taron dandalin manyan jami’ai kan dabarun fasalta makomar kasashe mambobin kungiyar yankin Sahel AES da ya gudana a birnin Ouagadougou na kasar Burkina Faso, ya dawo ga Nijar na karbar bakuncin zaman taron shugabannin rundunonin kasashen AES daga ranar Laraba 6 ga wata zuwa ranar Alhamis 7 ga watan Maris din shekarar 2024 a birnin Yamai.

Daga birnin Yamai, abokin aikinmu Mamane Ada ya aiko mana da wannan rahoto.

Makasudin wannan haduwa shi ne na sake duba da daidaita dabarun tsaro gaban kalubale na yanzu domin ‘yancin kasashen yankin Sahel.

Wannan taro ya gudana a gaban idon mambobin kwamitin ceton kasa na CNSP da manyan jami’ai na hedkwatocin rundunonin sojojin kasashen AES.

Tare da takwarorinsa na kasashen Burkina Faso da Mali, shugaban rundunar sojojin Nijar, birgadiye janar Moussa Salaou Barmo ya tunatar da cewa, rundunonin kasashen AES suna ci gaba da himmatuwa bisa manufarsu guda ta tabbatar da tsaro, zaman lafiya da kwanciyar hankalin kasashensu da al’ummominsu da ke yankin iyakoki uku.

Shugaban rundunar sojojin Nijar ya yi imani da cewa babu duk wani ci gaba mai karko da za’a samu idan babu zaman lafiya, kuma babban aikin da ya rataya ga wuyan sojojin mu shi ne musamman ma tabbatar da tsaron fadin kasashenmu daban daban, a cewarsa wannan nauyi ne da ya rataya kan wuyanmu domin tabbatar da kwanciyar hankali cikin kasashenmu. (Maman Ada)