logo

HAUSA

Wakilin NPC: Sabon Karfin Samar Da Hajoji Da Hidimomi Masu Karko Zai Samar Wa Duniya Damammaki

2024-03-08 13:59:06 CMG Hausa

 Shi Haofei, masanin kimiyya na cibiyar nazarin fasahar zamani maras gurbata muhalli ta Chongqing wadda ke karkashin inuwar kwalejin nazarin kimiyya ta kasar Sin ya bayyana cewa, sabon karfin samar da hajoji da hidimomi masu karko, ya alamta yadda ake samar da kayayyaki ta hanya mai inganci da babban mataki. Kuma ba za a iya samunsa ba, sai an yi kirkire-kirkiren fasahohin zamani.

Shi ya bayyana haka ne yayin da yake halartar taron shekara-shekara na majalisar wakilan jama’ar kasar Sin wato NPC a birnin Beijing, fadar mulkin kasar. Ya kuma bayyana cewa, sabon karfin samar da hajoji da hidimomi masu karko da kasar Sin take da shi, zai samar wa kasashen duniya sabbin fasahohi, da kayayyaki masu inganci, tare da samar musu damammaki da yawa a fannonin tsarin masana’antu da na harkokin cinikayya. (Tasallah Yuan)