logo

HAUSA

Munafuncin dodo ya kan ci mai shi kada Amurka ta shafawa kasar Sin bakin fenki

2024-03-07 13:57:09 CGTN HAUSA

 

An gudanar da taron menama labarai na taro na 2 na majalisar wakilan jama’ar Sin ta 14 a safiyar yau Alhamis, inda mamban ofishin siyasa na kwamitin kolin JKS, kana ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya amsa tambayoyin da aka yi masa game da manufofin diplomasiyya da Sin take dauka da huldarta da duniya.

Wang Yi ya ce, tattalin arzikin Sin ya samu karuwa bisa kashi 5.2% a bara, kuma ya taka rawa ga bunkasuwar duniya da kashi 1/3. Ya ce ba za a iya raba Sin da duniya ba idan ana maganar neman bunkasuwa, shi ya sa za a yi amai a lashe idan aka yada jita-jitar wai ana samun disashewar hasken kasar Sin.

Game da tsarin BRICS, a cewarsa, bunkasuwar kasashen BRICS na bayyana karfafa karfin kiyaye zaman lafiya, inda ya ce shigar da kasashe masu tasowa cikin harkokin duniya, muhimmin mataki ne na yiwa doka da odar duniya kwaskwarima.

Yayin da aka tabo maganar “tekun Nanhai”, Wang yi ya ce, Sin za ta kare ikonta bisa doka idan aka keta shi. Kuma ya yi gargadi da kakkausar murya, ga wasu kasashe wadanda ba su yankin “tekun Nanhai”, cewar kada su rura wutar ta da zaune tsaye a wannan yankin. (Amina Xu)