logo

HAUSA

Shugaban Senegal ya tsayar da ranar 24 ga watan Maris a matsayin ranar gudanar da zaben shugaban kasa da aka jinkirta

2024-03-07 09:55:13 CMG Hausa

Shugaban kasar Senegal Macky Sall, ya tsayar da ranar 24 ga watan Maris a matsayin sabuwar ranar da za a gudanar da zagayen farko na zaben shugaban kasar.

Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwar da majalisar ministocin kasar ta wallafa da yammacin jiya Laraba.

Sanarwar ta zo ne bayan majalisar kula da kundin tsarin mulkin kasar ta bayyana da yammacin jiya cewa, duk wata ranar zaben shugaban kasa bayan ranar 2 ga watan Afrilu, ta sabawa kundin tsarin mulkin kasar, kuma ba zai yiwu wa’adin shugaba mai ci ya zarce wannan lokaci ba.

Har ila yau, yayin taron majalisar ministocin, shugaba Sally ya sanar da rushe gwamnatin kasar tare da nada Sidiki Kaba a matsayin sabon firaministan da zai maye gurbin Amadou Ba. (Fa’iza Mustapha)