logo

HAUSA

Kasar Sin ta yi kira ga kasashen duniya su kyautata mu’amala da gwamnatin Taliban ta kasar Afghanistan

2024-03-07 14:17:00 CMG Hausa

Mataimakin zaunannen wakilin Sin a MDD Geng Shuang, ya yi kira ga kasa da kasa da su kyautata mu’amala da gwamnatin Taliban ta kasar Afghanistan.

Tun bayan kama mulkin Taliban a watan Augustan 2021, an samu kwanciyar hankali a kasar Afghanistan da ingantuwar tattalin arzikinta da zamantakewar al’umma da fadadar hadin kan yankunan kasar. Yana mai cewa wadannan ci gaba sun cancanci yabo. Ya kara da cewa, duk da haka, Afghanistan na fuskantar tarin kalubale a bangarorin jin kai da ci gaban tattalin arziki da barazanar ta’addanci.

A cewar Geng Shuang, ya kamata kwamitin sulhu ya kara fahimtar yanayin da Afghanistan ke ciki, ya tsara wata dabara mai ma’ana bisa yanayin kasar, ta yadda zai taka rawar da ta dace wajen raya ci gaban Afghanistan da dunkulewarta cikin al’ummar duniya. (Fa’iza Mustapha)