logo

HAUSA

Wang Yi: bai kamata a bambanta kasashe cikin harkokin diplomasiyya ba

2024-03-07 11:55:14 CMG Hausa

A yayin taron manema labaru na zama na biyu na majalisar wakilan jama’ar kasar Sin karo na 14 da aka gudanar da safiyar yau Alhamis, mamban ofishin kula da harkokin siyasa na kwamitin tsakiya na jam’iyyar Kwaminis ta Sin kuma ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya amsa tambayoyin ’yan jarida na ciki da wajen kasar, kan manufofin diplomasiyya na kasar Sin da raya dangantakar dake tsakanin Sin da kasashen waje.

Game da ra’ayin kasancewar bangarori masu fada a ji daban daban, Wang Yi ya bayyana cewa, bai kamata a bi ra’ayin kasashe masu karfi, da bambanta kasashen duniya kan harkokin kasa da kasa ba, kamar sanya wasu kasashe a kan teburin cin abinci, amma sauran kasashe ba su hau ba. Ya ce ya kamata a tabbatar da dukkan kasashe sun shiga aikin raya huldar bangarori daban daban cikin adalci, da samun moriya tare, da taka muhimmiyar rawa ba tare da yin la’akari da karfin kasashen ba.

Game da rikicin zirin Gaza, Wang Yi ya bayyana cewa, tilas ne kasa da kasa su ingiza tsagaita bude wuta nan da nan, inda ya ce jama’ar zirin Gaza suna da hakkin yin rayuwa a duniya. Kuma Sin ta na goyon bayan Palesdinu ta zama mamban MDD.

Game da dangantakar dake tsakanin Sin da Turai kuwa, Wang Yi ya ce, idan Sin da Turai suka yi hadin gwiwar samun moriyar juna, to ba za a samu ta da rikici tsakanin rukunai a duniya ba.

Da aka tabo halin da ake ciki a mashigin tekun Taiwan, Wang Yi ya bayyana cewa, tilas ne a yi adawa da batun ballewar yankin Taiwan daga kasar Sin, yana mai cewa hakan ne zai tabbatar da zaman lafiya a yankin. (Zainab Zhang)