logo

HAUSA

Firaministan kasar Malaysia ya ce bai kamata ba a yi tsoron bunkasuwar kasar Sin

2024-03-07 10:49:21 CMG Hausa

Firaministan kasar Malaysia Anwar Ibrahim, ya zargi kasashen yammacin duniya da yunkurin tilastawa sauran kasashe zabar wani bangare ko kulla kawance.

Anwar Ibrahim ya bayyana haka ne a ranar 4 ga wannan wata, bayan ganawar da ya yi da takwaransa na kasar Australia Anthony Albanese, yayin taron koli na musamman tsakanin mambobin kungiyar ASEAN da Australia na shekarar 2024 a birnin Melbourne na kasar Australia.

A cewar firaminista Anwar, Malaysia kasa ce mai cikakken ’yancin kai, kuma ba ta bin ra’ayin wata kasa ko zama karkashin sarrafawa. Ya ce duk da cewa kasar Malaysia ta kiyaye dangantakar abota dake tsakaninta da Amurka da Turai da Australia, bai kamata su hana Malaysia raya dangantakar abokantaka da makwabciyarta kasar Sin ba. Ya kara da cewa, idan wasu sun samu matsala da kasar Sin, bai kamata su tilasta  Malaysia ta shiga ciki ba, saboda kasar Malaysia ba ta da matsala da kasar Sin. (Zainab Zhang)