logo

HAUSA

LeBron James ya zamo dan wasan NBA na farko da ya kai ga samun maki 40,000 a kwallon kwando

2024-03-07 21:24:12 CMG Hausa

LeBron James dan wasan kwallon kwando na kungiyar Los Angeles Lakers, ya zamo dan wasan NBA na farko da ya kai ga samun maki 40,000 a tarihin kwallon kwando.

LeBron James, ya cike yawan makin ne yayin da suka tashi wasan ranar Asabar din karshen mako da kungiyar Denver Nuggets da maki 124 da 114, a filin wasa na Crypto.com dake birin Los Angeles.

Mintuna 10 da dakika 39 suka rage a tashi wasan James ya samu makin sa na 40,000, inda nan take magoya bayan sa suka barke da shewa, suna nuna murnar wannan nasara da gwanin su ya samu. Da kuma wannan nasarar dan wasan mai shekaru 39 da haihuwa, ya zamo dan wasan NBA na farko a tarihi da ya samu maki har 40,000, da makin kwallayen da ya ci bayan kubucewar kwallo daga wani dan wasan na daban har 10,000, da kuma tallafawa wajen cin kwallaye 10,000.

Yanzu haka dai LeBron James ya sha gaban gwarzon dan wasan kwallon kwando mafi cin kwallaye, wato Kareem Abdul-Jabbar wanda ya kai ga samun maki na 39,387 a watan Fabarairun da ya gabata. Kuma a wasan na karshen mako LeBron ya samu maki 26, ya café kwallayen da suka kubuce 4, kana ya taimaka wajen cin wasu kwallayen 9, inda ya kai ga kammala wasan da jimillar maki 40,017.

James yana cikin kakar wasan sa ta 21, kuma ba bu wani dan wasan kwallon kwando da ya yi kusa da shi a samun maki. Alkaluma sun nuna cewa, cikin ‘yan wasan dake biye da James akwai Kevin Durant na kungiyar Phoenix Suns, wanda ke matsayi na 9 a jerin ‘yan wasan kwando mafiya jefa kwallo a raga, kuma wanda a yanzu ke da jimillar maki 28,342.

Ghana ta kaddamar da babban wurin gudanar da gasar kasashen Afirka karo na 13

Mataimakin shugaban kasar Ghana Mahamudu Bawumia, ya kaddamar da filin wasan da zai zamo jigo, wajen gudanar da gasa ta 13 ta kasashen nahiyar Afirka dake tafe nan gaba cikin watan nan na Maris.

Filin wasan mallakin jami’ar Ghana, na iya daukar ‘yan kallo 11,000, yana kuma kunshe da dukkanin kayayyakin da ake bukata domin gudanar da wasannin ciki da wajen filin wasa. Kaza lika a filin ne za a gudanar da bikin budewa da rufe gasar.

Da yake tsokaci yayin kaddamar da filin, Bawumia ya ce a lokacin da Ghana ta samu albishir na amincewa da ba ta damar karbar bakuncin gasar, ba ta da cikakkun kayan da ake bukata, wanda hakan ya matsawa gwamnati lamba, ta kuma tashi tsaye wajen gina sassan da ake bukata, domin cimma nasarar karbar bakuncin wannan muhimmiyar gasa a karon farko a tarihin ta.

Mataimakin shugaban kasar ta Ghana, ya kara da cewa, gwamnatin kasar ta yi aiki tukuru wajen samar da dukkanin ababen da ake bukata don ganin an gudanar da gasar dake tafe cikin nasara, mako guda kafin bude ta.

Ya ce "Kaddamar da filin wasannin na jami’ar Ghana, kari ne kan manyan matakai da Ghana ke dauka, na shirin karbar bakuncin wannan gasa ta kasashen Afirka cikin nasara, ‘yan kwanaki kafin bude ta".

A watan Fabarairun da ya gabata ne, shugaban kasar Ghana Nana Addo Dankwa Akufo-Addo, ya kaddamar da manyan zaurukan gudanar da gasar.

Za a bude gasar ta kasashen Afirka karo na 13 ne a ranar Asabar din karshen makon nan a birnin Accra, yayin da za a gudanar da wasu daga wasannin gasar a birnin Cape Coast dake daura da teku.

Ghana za ta kaddamar da manufar shugaban kasa ta raya wasan kwallon kafa

Shugaban kasar Ghana Nana Addo Dankwa Akufo-Addo, ya ce nan ba da jimawa ba, zai kaddamar da manufar shugaban kasa, ta raya harkar kwallon kafa tsakanin matasan kasar, ta yadda hakan zai samarwa kasar matasan ‘yan wasan kwallo masu hazaka da za su rika wakiltar kasar.

Shugaba Akufo-Addo, ya bayyana hakan ne yayin da yake yiwa majalissar dokokin kasar jawabi kan halin da kasar ke ciki a shekarar nan ta 2024. Ya ce yana fatan manufar za ta gyara matsalar da aka samu a fannin kwallon kafar Ghana, musamman koma bayan da kungiyar kwallon kasar ta maza wato “Black Stars” ta gamu da shi.

A cewar shugaban na Ghana manufar za ta zakulo, da gina, da kuma horas da matasan ‘yan kwallo da za su shiga kungiyar kasar.

Ya ce "Gasar cin kofin Afirka ta baya bayan nan da Kwadebuwa ta lashe, kusan ta nuna matukar gazawar kungiyar Black Stars, ta kuma jefa ‘yan kasar cikin bakin ciki. Ina da imanin cewa, lokaci ya yi da za mu dauki matakan shawo kan wannan matsala”.

Har ila yau shugaban na Ghana, ya ce manufar da za a fitar za ta yaukaka hadin gwiwa tsakanin sassan wasanni na makarantu, da sashen bunkasa wasanni na ma’aikatar ilimin kasar, ta yadda za su rika aiki tare da hukumar wasan kwallon kafa ta Ghana, har a kai ga gina kungiyoyin wasanni na gundumomi, da yankuna da tawagar kasa mai karfi, ta maza da ta mata.

Ghana dai ta gamu da koma baya a fannin kwallon kafa a shekarun baya bayan nan, inda kungiyar kasar wato “Black Stars” ta fice daga gasar AFCON ta Afirka tun a wasannin rukuni, kamar yadda ta fuskanci irin wannan rashin nasara a gasar ta 2021.

Kasar Kamaru ta yanke kwangilar da ta kulla da kocin kwallon kafarta

Hukumar kwallon kafar kasar Kamaru ko (FECAFOOT), ta ce ta yanke kwangilar horas da tawagar ‘yan wasan kasar da ta kulla da koci Rigobert Song. Cikin wata sanarwa da babban sakataren hukumar ta FECAFOOT Blaise Djounang ya fitar, hukumar ta godewa Song da mataimakansa bisa jajircewar su wajen bautawa kasar Kamaru, ko da yake bai bayyana dalilan da suka sanya aka katse kwangilar kocin ba.

Blaise Djounang ya ce "cikin kwanaki kadan masu zuwa, za a sanar da tsarin daukar sabon mai horas da ‘yan wasan kungiyar ta “Indomitable Lions”, tare da masu taimaka masa.

Koci Song, wanda ya taba kasancewa kyaftin din kungiyar kwallon kafar Kamaru, kuma yake horas da ‘yan wasan kasar tun daga shekarar 2022, ya taimakawa kungiyar ta “Indomitable Lions” wajen samun gurbin buga gasar Qatar, ta cin kofin kwallon kafa na duniya wanda hukumar FIFA ke shiryawa, jim kadan bayan kama aikin sa.

To sai dai kuma a cewar masu nazarin kwallon kafar Kamaru, ba bu wani abun azo a gani da ya cimma, cikin shekaru biyu na kwangilar da ya kulla da hukumar wasan kwallon kafar kasar, in ban da wasanni 6 da ya yi nasara cikin wasanni 23 da ya jagoranci kungiyar ta “Indomitable Lions”.