Wang Yi: Aikin diplomasiyyar Sin na taka rawar gani ga duniya
2024-03-07 14:06:36 CGTN HAUSA
An gudanar da taron manema labarai na taro na 2 na majalisar wakilan jama’ar Sin ta 14 da safiyar yau Alhamis, inda mamban ofishin siyasa na kwamitin kolin JKS, kana ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya amsa tambayoyin da aka yi masa game da manufofin diplomasiyya da Sin take dauka da huldarta da duniya.
Wang Yi ya ce, a shekarar bara, Sin ta gudanar da ayyukan diplomasiyya bisa ruhin babban taron wakilan JKS karo na 20 karkashin jagorancin kwamitin kolin JKS, da shugaba Xi Jinping ke jan ragamarsa. Matakin da ya ce, ya taka rawa irin ta kasar Sin wajen kiyaye dunkulewa da hadin kan duniya, da ma gabatar da manufar Sin wajen magance rikici da kalubaloli daban-daban. Haka kuma ya taka rawa wajen ingiza zaman lafiya da samun bunkasuwar duniya baki daya, da ma kafa sabon yanayin tunani da matakai dangane da aikin diplomasiyya.
A cewarsa, har zuwa yanzu, tunanin raya kyakkyawar makomar bil Adama ta bai daya da Xi Jinping ya gabatar, ya samu bunkasuwa daga wani ruhi zuwa wani tsari na gaskiya, kuma daga shawarar Sin zuwa matsaya daya da duniya ta amince da ita, kana daga kyakkyawar fata zuwa ainihin ci gaban da ake samu, abin da ya bayyana kuzari da karfinsa. Yana mai cewa, an shigar da shi cikin kudurin babban taron MDD da na SCO da BRICS da sauran kungiyoyi sau da dama.
Yayin da aka tabo maganar huldar Sin da Amurka, Wang Yi ya ce, Sin ta dade tana nacewa ga manufofin da ta kan dauka kan kasar Amurka ba tare da sauyawa ba, ya kuma kalubalanci Amurkar da ta kyautata tunaninta game da bunkasuwar Sin, ta kuma cika alkwarin da ta yi.
Game da huldarta da Rasha, Wang Yi ya yi nuni da cewa, kasashen biyu na kafa wani sabon abin koyi a bangaren huldar kasa da kasa, wanda ya bambanta da ta lokacin yakin cacar baka. Kuma bangarorin biyu za su kiyaye tsarin kasa da kasa bisa kundin mulkin MDD, da kiyaye zaman lafiya da karko a shiyya-shiyya da duniya baki daya. (Amina Xu)