logo

HAUSA

Ministan wajen kasar Sin ya yi bayani kan manufofi da dangantakar Sin da kasahen waje

2024-03-07 10:49:33 CMG Hausa

A yau Alhamis, ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya kira taron manema labarai a gefen zama na biyu na taron Majalisar Wakilan Jama’ar Kasar Sin karo na 14.

Taron manema labaran ya mayar da hankali ne kan manufofi da dangantakar kasar Sin da kasashen ketare, inda Minista Wang Yi ya ce yayin da duniya ke cikin wani yanayi mai sarkakiya da sauye-sauye, Kasar Sin za ta zama wani karfi dake ingiza tabbatuwar zaman lafiya da kwaniciyar hankali da ci gaba a duniya. (Fa’iza Mustapha)