logo

HAUSA

Xi ya jaddada zurfafa gyare-gyare don inganta kwarewa a sabbin fannoni

2024-03-07 21:07:00 CMG Hausa

Shugaban kasar Sin Xi Jinping a yau Alhamis ya yi kira ga dakarun kasar da su karfafa alkiblar aikinsu, da zurfafa gyare-gyare da habaka kirkire-kirkire, don inganta kwarewarsu a sabbin fannoni.

Xi, ya bayyana hakan ne yayin da yake halartar taron tawagar sojojin ‘yantar da jama’a da kuma rundanar ‘yan sandan kasar a zama ta biyu ta majalisar wakilan jama’ar kasar Sin karo na 14, wato majalisar dokokin kasar. 

‘Yan majalisar shida daga cikin sojoji sun yi jawabi a wurin taron kan batutuwan da suka hada da kwarewar tsaro ta yanar gizo da kuma amfani da na’urori masu kwaikwayon tunanin dan Adam don bunkasa kwarewar aiki da makaman yaki masu sarrafa kansu.

Xi ya ce, yunkurin kasar Sin na hanzarta samar da sabon karfin samar da hajoji da hidimomi masu karko, ya ba damammaki da ba safai ake samun su wajen bunkasa kwarewa a sabbin fannoni masu tasowa ba.

Xi ya kara da cewa, ya zama dole a kara yin kirkire-kirkire masu zaman kansu kuma na asali, don samar da sabon karfin samar da hajoji da hidimomi masu karko da sabuwar kwarewar yaki. (Yahaya)