logo

HAUSA

Binciken CGTN: Sama da kashi 80% na masu amsa tambayoyi a duniya sun yaba da manufar harkokin waje na Sin

2024-03-07 20:13:45 CMG Hausa

Kwanan baya, tashar talabijin ta kasa da kasa ta CGTN ta babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin (CMG) ta hada kai tare da jami'ar Renmin ta kasar don fitar da wani binciken jin ra’ayin jama’ar duniya ta hanyar cibiyar nazarin sadarwa ta kasa da kasa ta sabon zamani, wato New Era International Communication Research Institute, inda aka nuna cewa, sama da kashi 80% na wadanda suka amsa tambayoyin binciken a duniya sun yaba da manufar harkokin wajen kasar Sin mai lumana kuma mai cin gashin kanta, a ganin su, hakan zai taimaka wajen samar da tsarin kasa da kasa mai adalci yadda ya kamata.

An gudanar da binciken ne a tsakanin mutane 31,980 a duniya, ciki har da na kasashen da suka ci gaba kamar Amurka, Jamus, Faransa, da Japan da sauransu, da kuma na kasashe masu tasowa irin su Mexico, Thailand, da Najeriya da dai sauransu.

A cikin wadanda suka ba da amsa, 91.1% daga cikinsu sun nuna yabo sosai game da jerin nasarorin da aka cimma bisa ga shawarar “Ziri daya da hanya daya” a cikin shekaru goma da suka gabata. Kana kashi 82.5% daga cikinsu suna ganin cewa, manufar “gina al’umma mai kyakkyawar makoma ga daukacin bil-Adam” ta kara azama mai dorewa ga kafa kyakkyawar makoma ga bil-Adam, tare da nuna madaidaiciyar hanyar da ya kamata dan Adam su bi. Baya ga haka, kashi 84.5% daga cikinsu sun yarda da ainihin manufar shirin ci gaban duniya, kuma sun yi imanin cewa ci gaba shi ne hanyar magance matsalolin kasa da kasa da tabbatar da jin dadin zaman rayuwar jama’a. Kashi 85.6% na masu amsar sun yi imanin cewa, tsaro shi ne muhimmin abun da ake bukata don samun ci gaba, kuma ya kamata kasashe daban daban su yi aiki tare don gina daidaitaccen tsarin tsaro mai inganci da dorewa.

Bisa binciken kuma, a ganin kashi 76.2% na masu amsa tambayoyi, manufar harkokin wajen kasar Sin ta kiyaye moriyar kasar yadda ya kamata, kana kashi 65.3% na masu amsa tambayoyin sun yi imanin cewa, yadda kasar Sin ke taka rawa a harkokin duniya ya kawo tabbaci da kwanciyar hankali ga kasashen duniya. (Mai fassara: Bilkisu Xin)