logo

HAUSA

An bude taron makamashi na "Africa Energy Indaba 2024"

2024-03-06 15:51:05 CMG Hausa

An bude dandalin tattauna ajandar nahiyar Afirka game da samar da isasshen makamashi da sauya akalar amfani da shi ko "Africa Energy Indaba 2024", a birnin Cape Town na Afirka ta Kudu.

Taron wanda aka bude a jiya Talata, ya hallara mutane sama da 4,000, kuma taken sa shi ne "Sauya tafiyar Afirka game da makamashi daga buri zuwa aiki; Samar da makoma mai dorewa da karko."

Ana fatan mahalarta taron karo na 16, za su tattauna game da dabarun ingiza ajandar samar da makamashi ta duniya, da kawar da matsalar kamfar sa a sassan nahiyar Afirka.

Da yake gabatar da jawabin kaddamar da taron, ministan ma’aikatar albarkatun kasa da makamashi na Afirka ta Kudu Gwede Mantashe, ya ce manufar ita ce lalubo dabarun sauya matsayar Afirka, daga yanayin fitar da dimbin iskar carbon mai dumama yanayi zuwa mafi karancin hakan.

A nata bangare kuwa, babbar daraktar dandalin na "Africa Energy Indaba" Liz Hart, cewa ta yi ya zama wajibi kasashen Afirka su samar da nasu tafarkin, na sauya salon amfani da nau'o'in makamashi.

Taron na wannan karo ya samu halartar ministocin wasu kasashen Afirka, da masu zuba jari, da kwararru daga masana'antu da kuma masu amfani da makamashi. (Saminu Alhassan)