logo

HAUSA

Sin ta bukaci Isra'ila ta daina kaskantar da batun kafa kasashe biyu

2024-03-06 10:26:06 CMG Hausa

Mataimakin jakadan kasar Sin na dindindin a MDD Geng Shuang, ya bukaci Isra’ila ta daina kaskantar da batun kafa 'yantattun kasashe biyu.

Da yake tsokaci kan amfani da kujerar naki a Kwamitin Sulhu na MDD, Geng Shuang ya bayyanawa babban taron MDD cewa, suna bukatar Isra’ila ta daina lahantawa da kaskantar da batun kafa kasashe biyu, haka kuma ta daina mamayar da ta sabawa doka.

Wakilin na Sin ya nanata cewa, kusan watanni 5 kenan da barkewar rikicin Gaza, amma Amurka ta yi amfani da karfi wajen toshe kiran kwamitin sulhu na tsagaita bude wuta har sau 4, lamarin da Sin ke gani a matsayin abun kunya.

Ya kara da cewa, sakamakon kuri'ar da kwamitin sulhun ya kada, ya nuna a bayyane cewa, mafi rinjayen mambobin kwamitin sun amince da bukatar dakatar da bude wuta a Gaza.

Sai sai, Amurka ta kasance kasa daya tilo da take amfani da karfin kujerar naki wajen kawo tsaiko ga matsayar majalisar, lamarin da ya haifar da rashin gamsuwa daga al'ummomin duniya. (Fa'iza Mustapha)