logo

HAUSA

Yadda Kasar Sin Take Kokarin Bunkasa Tattalin Arziki Irin Na Zamani

2024-03-06 14:05:58 CMG Hausa

Domin ci gaban tattalin arziki na zamani, dole ne mutane su shirya canza halayensu, tare da daidaita akidunsu bisa tafarkin ci gaba, da saka hannun jari kan sabbin fasahohi. Cije wa wuri guda da rashin son sauyi na kawo cikas ga bunkasuwa. La’akari da wannan ne kasar Sin ta kaddamar da dabarun yin gyare-gyare da bude kofa ga kasashen waje. Idan muka waiwayi sauye-sauyen da kasar Sin ta samu, dole ne mu gane cewa tsohon tsarin bunkasa tattalin arziki ya kawo karshe yayin da ta rungumi sabbin tsare-tsaren bunkasa tattalin arzikinta daidai da bukatar zamani ta hanyar zuba jari da habaka sassan tattalin arziki masu muhimmanci da fannonin hidima na zamani, wadanda suka hada da kiwon lafiya, ilimi, sufuri, sadarwa ta dijita, kirkirarriyar basira wato AI, hada-hadar kudi, dabarun aiki, kayayyakin more rayuwa masu dorewa na birane da sabbin tsarin abinci da amfanin kasa. 

Firaministan kasar Sin Li Qiang ya gabatar da rahoton aikin gwamnati a taron wakilan jama’ar kasar Sin NPC a babban zauren taron jama’a a jiya Talata inda ya bayyana irin kokarin da kasar take yi wajen bunkasa tattalin arzikinta daidai da zamani, kuma cikin yanayi mai kyau da armashi, inda ma’aunin GDPn kasar ya zarce Yuan triliyan 126, adadin da ya karu da kaso 5.2 bisa dari. 

Idan ana maganar tattalin arziki ta zamani dole a tabo batu gina sabbin makamashi mara gurbata muhalli wanda kasar Sin ta ciri tuta wajen samar da kayayyaki masu amfani da makamashi mai tsafta mara gurbata muhalli. Alal Misali, Sabbin Zakaru guda Uku wato kayayyakin sassan makamashin hasken rana wanda a halin yanzu kasar Sin ke rike da kashi 50 cikin dari na kasuwar sa a duniya, da matoci masu amfani da sabbin makamashi wanda a bara ta fitar da guda miliyan 1.2 wato karuwar kashi 77.6 cikin dari, da batirin lithium inda kamfanonin kasar Sin guda shida ke cikin jerin manyan kamfanoni goma na duniya da ke samar da shi. Wadannan sabbin zakaru guda uku suna ba da gagaruwar gudummawa wajen rage tasirin sauyin yanayi tare da bunkasa tattalin arziki kasar Sin

Tattalin arzikin kasar Sin ta taka muhimmiyar rawa a bara duka da cewa a tattalin arzikin duniya baki daya ya fuskanci tafiyar hawainiya, godiya ga tsare-tsare da nagartattun manufofin kasar wadanda suka kasance rigakafi ga kalubolin da ka iya dakushe tattalin arzikin yayin da yawan motocin da kasar Sin ta siyar ya kai miliyan 30.1 wanda ya ninka na Amurka, Yawan danyen karafa da kasar Sin ta samar ya kai sama da tan biliyan 1.02 ya ninka na Amurka sau 12.6, kuma adadin aikin gina jiragen ruwa da kasar Sin ta kammala ya kai nauyin tan miliyan 42.32 wanda ya ninka na Amurka fiye da sau 70. Wadanna nasarorin na nuni da karfi da ci gaban tattalin arzikin Sin. (Sanusi Chen, Mohemmed Yahaya, Saminu Alhassan)