logo

HAUSA

Sin da Aljeriya na fatan bunkasa hadin gwiwar raya tattalin arziki

2024-03-06 10:47:37 CMG Hausa

Manyan jami'ai da wakilai daga kasashen Sin da Aljeriya, sun hallarci dandalin raya tattalin arziki a birnin Setif na gabashin kasar Aljeriya.

Taron na jiya Talata, wanda ofishin jakadancin Sin a Aljeriya da gwamnatin lardin Setif suka jagoranta, ya samu halartar jami’ai da wakilai 260, ciki har da 'yan majalissar Aljeriya da jami'an gwamnatin kasar, da kuma 'yan kasuwa daga kasashen biyu.

Cikin jawabin da ya gabatar yayin taron, jakadan Sin a Aljeriya Li Jian, ya ce cikakkiyar dangantakar abokantaka ta hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare tsakanin Sin da Aljeriya ta shiga sabon matsayi, kuma hadin gwiwar raya tattalin arziki da cinikayya tsakanin sassan biyu ya kara bunkasa, inda a karon farko a shekarar 2023 da ta gabata, darajar cinikayya tsakanin kasashen biyu ta haura dalar Amurka biliyan 10.

A nasa bangare kuwa, gwamnan lardin Setif Mustapha Limani, cewa ya yi, "Mun gayyace ku nan ne domin karfafa, da bunkasa hadin gwiwa karkashin tsarin cin gajiyar juna a fannonin cudanyar tattalin arziki, da yaukaka wadata, da ci gaban al'ummun kasashen Sin da Aljeriya."  (Saminu Alhassan)