logo

HAUSA

Sin ta yi kira ga kasashen duniya da su tallafawa matakan siyasa a Sudan ta Kudu

2024-03-06 09:55:42 CMG Hausa

Babban jami'i a ofishin wakilcin Sin na MDD Dai Bing, ya yi kira ga kasashen duniya da su tallafawa matakan siyasa a kasar Sudan ta Kudu, kana su goyawa kasar baya wajen karfafa kwarewar ayyuka a fannin wanzar da tsaro.

Dai Bing ya bayyana hakan ne a jiya Talata, yayin taron kwamitin tsaron MDD da ya gudana. Ya ce bana shekara ce mai matukar muhimmanci ga Sudan ta Kudu, musamman a fannin ingiza matakan mika mulki, da samar da ci gaban kasar cikin lumana. Ya ce Sin na ganin ya dace sassan kasa da kasa su fadada tallafin su ga kasar. Kuma a nata bangare, Sin na goyon bayan bangarorin Sudan ta Kudu, a yunkurin su na gaggauta aiwatar da yarjejeniyar zaman lafiya, da matakan tsawaita wa'adin gwamnatin rikon kwaryar kasar, ta yadda za a kai ga samar da kyakkyawan yanayin mika mulki ga zababbiyar gwamnatin farar hula, tare da gudanar da babban zabe.

Kaza lika Dai Bing ya kara da cewa, Sin na goyon bayan hadin gwiwar kungiyar tarayyar Afirka ta AU, da ta raya gabashin Afirka IGAD, da MDD, wajen samar da karin tallafin bunkasa harkokin siyasa a Sudan ta Kudu.  (Saminu Alhassan)