An cika kwanaki 1000 da fara aiki da layin dogon Lagos-Ibadan
2024-03-06 21:14:55 CMG Hausa
A jiya ranar 5 ga watan Maris ne aka cika kwanaki 1000 da fara aiki da layin dogon Lagos-Ibadan. A watan Yunin shekarar 2021 ne, an kaddamar da layin dogon da kamfanin CCECC na kasar Sin ya gina, layin dogon da ke da tsawon kilomita 157 da ma wani reshensa mai tsawon kilomita 7, wanda ke iya gudu da saurin kilomita 150 cikin sa’a guda. Kawo yanzu layin dogon ya yi zirga-zirgar fasinjoji sama da miliyan biyu, wanda ba kawai ya saukaka zirga-zirgar al’umma ba, har ma ya inganta ayyukan jigilar kayayyaki tsakanin tashoshin jiragen ruwa da sauran sassan kasar.