logo

HAUSA

Sabbin fasahohin na kara inganta masana'antar kera motoci ta kasar Sin

2024-03-06 21:23:49 CMG Hausa

Kasar Sin ta bayyana Sabon karfin samar da hajoji da hidimomi masu karko a matsayin aikinta da ta fi mayar da hankali na tattalin arziki a shekarar 2024, wanda ya jaddada muhimmancin ci gaban kimiyya da fasaha da yin kirkire-kirkire wajen inganta ci gaban tattalin arziki da zaman al’umma. Kamfanin kera motoci na kasar Sin NIO ya samu nagartaccen inganci wajen samar da kaya ta hanyar yin kirkire-kirkire da amfani da tsarin sarrafa kansa.