logo

HAUSA

Mu ne wakilan jama'a

2024-03-05 22:00:22 CMG Hausa

A yau Talata ne aka bude taron shekara-shekara na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin. Wannan babban batu ne ga al’ummar Sinawa a rayuwar siyasarsu.

Wakilan majalisar wakilan jama'ar kasar Sin kusan 3000 daga wurare daban daban na kasar sun tattaru a birnin Beijing, don tattauna harkokin kasar.

Ga wannan bidiyo da muka tsara, domin kallon yadda wakilan majalisar wakilan jama'ar kasar Sin su uku suke gudanar da ayyukansu, da kuma mayar da muradun jama’a matsayin muradun kasa.