logo

HAUSA

Rahoto: Kamfanonin gwamnati da masu zaman kansu da masu jarin waje na da muhimmanci ga zamanantar da kasar Sin

2024-03-05 10:58:53 CMG Hausa

Wani rahoton gwamnati da aka gabatarwa majalisar wakilan jama'ar kasar Sin a yau Talata, ya bayyana cewa, kamfanonin da suka hada da na gwamnati da masu zaman kansu da masu jarin waje, dukkansu muhimman karfi ne dake ingiza zamanantar da kasar Sin.

Rahoton, wanda ya lashi takobin nacewa manufar zurfafa gyare-gyare, ya ce kasar Sin za ta yi kokari wajen bunkasa kuzarin dukkanin harkokin kasuwanci. Haka kuma, kasar za ta samar da karin kamfanonin da suka kai matsayin kasa da kasa, tare da aiwatar da ka'idojin da za su saukaka ci gaban bangarori masu zaman kansu da matakan da suke taimaka musu.

Bugu da kari, kasar Sin za ta samar da wani ingantaccen tsarin gaggauta gina wata kasuwar bai daya ta kasa, kana za a kara daidaita ka'idoji da cibiyoyi masu ruwa da tsaki a bangaren kare hakkin mallakar fasaha, da samar da damar shiga kasuwa, da takara cikin adalci, da tabbatar da sahihancin kamfanoni da sauransu. (Fa'iza Mustapha)