logo

HAUSA

An bude taro karo na 2 na majalisar NPC ta 14 a Beijing

2024-03-05 09:17:19 CMG Hausa

Da misalin karfe 9 na safiyar yau Talata ne aka bude taro karo na 2 na majalisar wakilan jama’ar kasar Sin ta 14 a babban zauren taruwar jama’a dake birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin. Babban sakataren kwamitin tsakiyar Jam’iyyar Kwaminis ta Kasar Sin, kana shugaban kasa, shugaban kwamitin soja Xi Jinping, da manyan jami’an JKS, da na gwamnatin kasar sun halarci bikin bude taron. (Maryam)