logo

HAUSA

An Bude Taron Majalisar Wakilan Jama’Ar Kasar Sin A Beijing

2024-03-05 11:19:07 CGTN HAUSA

Yau Talata da karfe 9 na safe, aka bude taron majalisar wakilan jama’ar Sin a babban dakin taron jama’ar Sin dake nan birnin Beijing. Wakilai kimani 3000 daga wurare da kabilu da sana’o’i daban-daban ne suke halartar taron, don sauke nauyin dake wuyansu na tsarin mulki da shari’a da dokoki.

Majalisar wakilan jama’ar Sin mai wa’adin shekaru 5, hukumar koli ce a bangaren mulkin kasar. Ana gudanar da taron majalisar ne a ko wace shekara, inda ake tattaunawa da kuma yanke shawara kan manyan manufofi da dokoki da nada jami’ai. Haka kuma, matakin koli ne da jama’ar Sin suke shiga harkokin kasa, lamarin dake bayyana manufar gudanar da siyasa ta dimokuradiyya a cikin tsarin mulki na gurguza mai sigar musamman na kasar Sin. Wannan taron dake gudana, ya kasance taro na biyu na majalisar wakilan jama’ar Sin karo na 14, wanda zai tattauna tare da nazari kan sabon rahoton ayyukan gwamnati, hakan ya sa yake jan hankalin bangarorin daban-daban.

Yayin taron na wannan karo mai wa’adin mako daya, wakilan jama’ar Sin za su saurari rahotannin gwamnatin tare da tattaunawa da gudanar da bincike, da kuma takaita ci gaban da aka samu a bara, da tsai da tafarkin raya kasa a sabuwar shekara. A sa’i daya kuma, taron zai yi bincike kan rahoton bunkasuwar tattalin arziki da al’ummar kasar, da rahoton kasafin kudi na kwamitin tsakiya da na wuraren daban-daban, har ma da rahoton aiki na kotun koli da na hukumar koli ta bin bahasi ta jama'ar kasar.(Amina Xu)