logo

HAUSA

Shamsuddeen Lawal: Zan yi kokarin karfafa hadin-gwiwar Najeriya da Sin a fannin makamashi

2024-03-05 15:39:05 CMG Hausa

Shamsuddeen Lawal, dan Katsina ne daga tarayyar Najeriya, wanda a yanzu haka yake karatun digiri na uku a wata jami’a mai suna Harbin Engineering University dake birnin Harbin na lardin Heilongjiang na kasar Sin.

Kwanan nan ne Murtala Zhang ya zanta da malam Shamsuddeen Lawal, inda ya bayyana ra’ayinsa kan ci gaban kasar Sin, da wasu al’adun da suka burge shi a kasar.

Shamsuddeen ya kuma yi karin haske kan bangaren karatun da yake nazari yanzu a kasar Sin, da bayyana burinsa na amfani da ilimin da ya samu a kasar, don amfanawa al’ummar Najeriya. (Murtala Zhang)