logo

HAUSA

Wata tawagar manyan jami’an kasar Nijar na ziyarar aiki a kasar Benin

2024-03-05 09:52:44 CMG Hausa

Wata babbar tawaga ta jami’an kwastam ta Nijar ta isa ranar Lahadi a birnin Cotonou domin wata ziyarar aiki da ta fara daga ranar 3 har zuwa ranar 8 ga watan Maris, wata alama ta daidaituwar dangantaka tsakanin kasashen biyu.

Daga birnin Yamai, abokin aikimu Mamane Ada ya aiko mana da wannan rahoto. 

Ita wannan tawaga tana kunshe da manyan jami’an kwastam na Nijar, ’yan kasuwa da wasu kwararru duk a karkashin jagorancin kanal Abdoulaye Maiga, darektan kula da daidaita al’amura da saukaka tattalin arziki. 

A cewar bayanan da suka fito, wannan ziyarar aiki ta manyan jami’an Nijar bayan janye takunkumin kungiyar CEDEAO na da nasaba da shirin bututun mai na WAPCO da aka kaddamar da shirin aikinsa a ranar 1 ga watan Maris din shekarar 2024.

Haka kuma a yayin wannan rangadi, tawagar kasar Nijar da hukumomin kasar Benin za su maida hankali wajen neman bakin zaren harkokin da suka shafi huldar kasuwanci tsakanin kasashen biyu, tun lokacin rufe iyakoki. Ganin cewa fiye da kwantena dubu 13 na kasar Nijar aka tsaida a kasar Benin, a cewar kungiyar ’yan kasuwa masu shigo da fitar da kayayyaki.

A rike cewa, kamfanin CNPC na kasar Sin ya samu kwangilar gina wannan bututun mai bisa tsawon kilomita dubu 2, wanda kusan kilomita 675 ya ratsa doron kasar Benin. 

Mamane Ada, sashen hausa na CMG daga Yamai a jamhuriyyar Nijar.