logo

HAUSA

Bai kamata a rasa “damar kasar Sin” ba

2024-03-05 21:49:15 CMG Hausa

Rahoton aikin gwamnati na shekara ta 2024 da aka gabatar don a duba shi a wajen taron majalisar wakilan jama’ar kasar Sin (NPC) a yau Talata 5 ga wata, yana jawo hankalin duk duniya.

Tattalin arzikin duniya na tafiyar hawainiya a halin yanzu, kuma akwai cibiyoyin kasa da kasa da dama da suka yi hasashen cewa, saurin karuwar tattalin arzikin duniya na bana ba zai wuce kaso 3 bisa dari ba. Ita dai kasar Sin ta tsara burinta dake cewa, karuwar yawan GDPn kasar zai kai kaso 5 bisa dari a shekarar da muke ciki, wanda ya yi daidai da na bara, kana, ya dace da hasashen bangarori daban-daban, tare da karfafa gwiwar duk duniya.

To, yaya za’a yi don cimma burin a zahirance? Gwamnatin kasar Sin ta tsara wasu muhimman ayyuka guda 10 a bana, ciki har da kara kokarin raya tsarin masana’antu irin na zamani, da zurfafa aiwatar da manufar raya kasa ta hanyar ba da ilimi, da fadada bukatun cikin gida, da habaka bude kofa ga kasashen waje da sauransu.

A halin yanzu, duniya na fuskantar matsaloli da dama, ciki har da tsanantar rikicin siyasa na shiyya-shiyya, da rashin karfin ci gaban tattalin arziki. Ba abu ne mai sauki kasar Sin ta cimma burinta na bana ba, dole ta rubanya kokari. Amma kamar yadda rahoton ya ce, abubuwa masu kyau sun fi marasa kyau yawa. Don haka, sabon ci gaban kasar Sin zai iya samar da sabbin damammaki ga duniya, wannan shi ne alkawarin da kasar ta dauka, kuma dole ya zama abun da kasar ta aikata a zahirance. (Murtala Zhang)