logo

HAUSA

Firaministan kasar Sin ya gabatar da rahoton aikin gwamnati

2024-03-05 11:06:48 CMG Hausa

Yau Talata, firaministan kasar Sin Li Qiang ya gabatar da rahoton aikin gwamnati a babban zauren taruwar jama’a, inda ya ce gabanin manyan kalubalolin da ake fuskanta a kasashen duniya, da muhimman ayyukan yin kwaskwarima, da neman ci gaba, da tabbatar da zaman karko a cikin gida, JKS a karkashin jagorancin shugaba Xi Jinping, ta hada kai da al’ummomin kabilu daban daban na kasar Sin, wajen warware matsalolin da suka gamu da su, yayin da suke sauke nauyinsu yadda ya kamata, kana sun cimma babbar nasara, da cimma burinsu a fannin raya tattalin arziki da zaman takewar al’umma.

A sa’i daya kuma, an cimma nasarar neman ci gaba mai inganci, da tabbatar da yanayin zaman karko na zamantakewar al’umma, lamarin da ya sa aka sami gagarumin ci gaba a fannin gina zamantakewar al’umma ta zamani bisa tsarin gurguzu a dukkanin fannoni.

Ya kuma kara da cewa, tattalin arzikin kasar ya bunkasa cikin yanayi mai kyau, inda ma’aunin tattalin arzikin GDPn ya zarce Yuan triliyan 126, adadin da ya karu da kaso 5.2 bisa dari. Kana, an samu ci gaba a fannin gina tsarin masana’antu na zamani, kuma masana’antun gargajiya sun samu kyautatuwa, yayin da sabbin sana’o’i suka bunkasa cikin sauri, kana, wasu manyan sakamakon da aka samu a fannin kirkire-kirkire sun kasance a sahun gaba tsakanin kasashen duniya.

Li Qiang ya kara da cewa, an samu sabbin sakamako a fannonin sabunta kimiyya da fasaha, kana, karfin yin kirkire-kirkire yana karuwa ba tare da tsayawa ba. A sa’i daya kuma, an zurfafa ayyukan yin kwaskwarima a gida da bude kofa ga waje yadda ya kamata, yayin da ake inganta tushen neman bunkasuwa cikin tsaro. Haka zalika kuma, ana kyautata muhallin hallitu cikin yanayin zaman karko, yayin da ake kiyaye zaman al’umma yadda ya kamata.

Bugu da kari, ya ce, ba abu ne mai sauki ba, samun bunkasuwar tattalin arziki cikin shekarar da ta gabata, bisa kokarin da dukkanin al’ummomin kasar suka yi a fadin kasar, ba kawai an cimma buri a fannin raya tattalin arziki ba kadai, har ma an samu gaggarumin ci gaba a harkoki da dama. Sakamakon da aka samu, ya nuna cewa, a karkashin jagorancin kwamitin tsakiyar JKS da shugaba Xi Jinping, jama’ar kasar Sin ta nuna karfi da basira waje warware kalubalolin dake gabanta. Tabbas ne, kasar Sin za ta sami ci gaba na dindindin, yayin da ake kara samun makoma mai haske. (Mai Fassarawa: Maryam Yang)