logo

HAUSA

Sin na fatan samun bunkasar tattalin arziki da kaso 5 bisa dari a 2024

2024-03-05 10:40:20 CMG Hausa

Rahoton ayyukan gwamnati da aka gabatar ga majalissar wakilan jama’ar kasar Sin domin tattaunawa a Talatar nan, ya nuna burin kasar Sin na bunkasa tattalin arzikin kasa a shekarar 2024 da kaso 5 bisa dari.

A cewar rahoton, Sin za ta kirkiri sama da ayyukan yi miliyan 12 a birane, tare da takaita alkaluman rashin aikin yi a biranen kasar kan kimanin kaso 5.5 a shekarar ta bana.

Kaza lika, Sin za ta yi aiki tukuru, wajen aiwatar da managartan manufofin kudi, da ci gaba da gudanar da tsare tsaren tsimin kudade, ta yadda za a tsayar da gibin ma’aunin GDPn kasar kan kaso 3 bisa dari, yayin da gibin kashe kudaden a bangaren gwamnati zai karu da kudin Sin yuan biliyan 180, kan wanda ke cikin kasafin kudin kasar na shekarar 2023.  (Saminu Alhassan)