logo

HAUSA

Kasar Sin ta bayyana ra'ayinta game da batun kare hakkokin bil adam a Geneva

2024-03-05 10:14:11 CMG Hausa

Jakadan dindindin na kasar Sin a ofishin MDD dake Geneva da sauran hukumomin kasa da kasa dake Switzerland, Chen Xu, ya yi bayani kan mahangar kasar Sin dangane da batun ingantawa da kare hakkokin bil adama, yana mai jaddada cewa, zaman lafiya da ci gaba, su ne tushen kare hakkokin bil adama.

Chen ya bayyana haka yayin taron majalisar kare hakkin dan Adam ta duniya karo na 55. A cewarsa, kare hakkin bil adama aiki ne na bai daya da ya rataya a wuyan dukkan al'ummomin duniya.

Da yake kira da a samu yanayi mai daidaito da ajiye bambance-bambance a gefe guda tare da kara aminci da juna, Chen Xu ya kuma yi kira da a hada hannu wajen yin adawa da tsoma baki cikin harkokin gidan kasashe ta hanyar fakewa da batutuwan hakkokin bil adama.

A cewarsa, kasar Sin na nacewa wajen bin tafarkin kare hakkokin bil adama da ya dace da yanayin kasar.

Ya kuma nanata kudurin kasarsa na hada hannu da masu ruwa da tsaki wajen kare hakkokin bil adama ta hanyar tabbatar da tsaro, da ci gaba da inganta kare hakkokin ta hanyar hadin gwiwa, da inganta burin duniya na raya ayyukan kare hakkokin bil adama. (Fa'iza Mustapha)