logo

HAUSA

Wani harin Israila a Gaza ya yi sanadin mutuwa da jikkatar gomman Falasdinawa

2024-03-04 09:51:54 CMG Hausa

Ma'aikatar lafiya ta yankin Gaza dake karkashin ikon kungiyar Hamas, ta ce gomman Falasdinawa sun mutu yayin da wasu suka jikkata, sanadiyyar harin Isra’ila a lokacin da suke jiran kayayyakin agaji a birnin Gaza.

Kakakin ma'aikatar Asraf al-Qedra ne ya bayyana cikin wata sanarwa da ya fitar a jiya Lahadi.

Wasu majiyoyin tsaro da na lafiya sun shaidawa Xinhua cewa, dakarun Isra'ila sun bude wuta kan mutane a shataletalen Kuwait, wanda ke kudu da birnin Gaza, a yayin da mutanen ke jiran manyan motocin agaji dake dauke da fulawa.

Rahoton gidan Talabijin na Falasdinu ya ruwaito cewa, da farko a jiya Lahadin, jiragen yakin Isra'ila sun kai hari kan wata karamar motar dakon kaya dake dauke da kayayyakin agaji a Deir al-Balah dake tsakiyar yankin Zirin Gaza, lamarin da ya yi sanadin kashe mutane a kalla 8.

Kawo yanzu dai bangaren Isra'ila ba ta ce komai ba dangane da aukuwar hare-haren. (Fa’iza Mustapha)