logo

HAUSA

Lu Yutong na bayar da gagarumar gudummawa wajen ci gaban kasar Sin a bangaren samar da Supercomputer

2024-03-04 16:31:34 CMG Hausa


Lu Yutong, daraktar cibiyar samar da kwamfutocin sarrafa bayanai ko lissafi da saurin gaske wato Supercomputer ta Guangzhou dake lardin Guandong na kudancin kasar Sin, kuma farfesa a kwalejin nazarin kimiyyar kwamfuta da Injiniya a jami’ar Sun Yat-sen. Lu ta sadaukar da kanta wajen taimakawa kasar Sin cimma gagarumar nasara na tsawon shekaru 10 a bangaren samar da kwamfutocin sarrafa bayanai da saurin gaske a duk fadin duniya. An nada Lu a matsayin shugabar kula da shirye-shriye na babban dandalin taro na ISC High Performance na shekarar 2019, wadda ta kafa tarihi a matsayin mace ta farko kuma basiniya ta farko, masaniyar kimiyya da ta kasance shugabar kula da shirye-shriye na babban dandalin.

A lokacin da Lu Yutong take aji na 4 a jami’a, tana da malami wanda shi ne ke da alhakin hada kwamfuta kirar Yinhe-2. Lu ta taimaka masa wajen gwaji da tantance tsarin aikin kwamfutar. Lu ta ce, “Ba kamar fasahohin kwamfuta na yanzu ba, sai da muka sanya manhajoji daya bayan daya. Wato idan muka yi kuskure, sai mun sake farawa daga farko. Dole sai da muka yi aikin cikin hakuri da nutsuwa. Saboda irin kulawa da aka nuna wa kwamfutar, masana kimiyya na kasar Sin sun samar da kwamfutar sarrafa bayanai da saurin gaske wato Supercomputer da kansu.”

A ranar 17 ga watan Yunin 2013, Tianhe-2 ta zama ta farko cikin jerin manyan kwamfutoci 500 mafiya sauri a duniya. Ta ci gaba da rike matsayin har zuwa Yunin 2016, lokacin da wata kwamfuta da masana kimiyya na kasar Sin suka samar ta fito ta zarce ta. Yayin da ake samar da ita, Lu wadda ita ce mataimakiyar mai tsara fasalin kwamfuta kirar Tianhe-2 tare da abokan aikinta, sun gamu da matsaloli. Ta jagoranci abokan aikinta wajen samun nasarori daya bayan daya a muhimman fannonin fasahohin Supercomputer. Domin inganta yanayin aikin kwamfutar, sun gudanar da daruruwan miliyoyin gwaje-gwaje cikin watanni 3. A yayin da suke mataki mafi muhimmanci na samar da kwamfutar, sun yi aiki tare domin warware wata matsalar fasaha mai muhimmanci.

Lu ta furta cewa, “abun da ya karfafa min gwiwa tare da abokan aikina wajen shawo kan kalubale a binciken kimiyya shi ne, ruhin kishin kasa da hadin gwiwa da jajircewa, wadanda dukka abubuwa ne da muka gada daga magabatan Sinawa masu binciken samar da Supercomputer. Ni da abokan aikina mu kan dage fiye da kima, kuma mun yi namijin kokari wajen samar da cibiyar samar da kwamfutocin Supercomputer da ya kai matsayin na kasa da kasa.”

Lu ta kan karfafawa matasa abokan aikinta gwiwar gudanar da nazari mai zurfi na ka’idoji da fasahohi ta hanyar bita, haka kuma su gabatar da ra’ayoyi mabambanta kan binciken da suke aiwatarwa. An karfafa musu gwiwar gabatar da ra’ayoyinsu da tantancewa da nazari da kansu, da kuma kokarin lalubo inda aka samu matsala a sakamakon binciken da suke gudanarwa, da kuma bayar da shawarwarin yadda za a inganta fasahohin.

A farkon shekarun 1990, Lu na amfani ne da kwamfutar kan teburi domin binciko bayanan fasahohin zamani dake da alaka da masana’antar samar da kwamfuta a wasu kasashe. Ta bayyana cewa, “Akwai yiwuwar ina daga cikin mutane na farko-farko da suka fara amfani da intanet a kasar Sin. Ko ka fita kasar waje ko a’a, za ka iya samun hanyoyin koyo da sanin abubuwan dake wakana a waje, haka kuma za ka iya kara fahimtarka game da harkokin duniya.”

Masu binciken samar da Supercomputer na kasar Sin, sun bayyana ra’ayoyinsu yayin wasu shirye-shiryen kara wa juna sani na kasa da kasa da aka yi a baya bayan nan, kuma shigarsu irin wadannan shirye-shirye ya sa sun kara yin fice a tsakanin masana lissafi irin na Supercomputer na duniya. Lu ta bayyana cewa, “yayin da kasarmu ke samun dimbin nasarorin fasaha, kuma karfin kasarmu ke karuwa, masana kimiyya na kasar Sin sun cimma kuma za su cimma nasarori da dama. Masu binciken Supercomputer na zamaninmu, za mu sadaukar da kanmu wajen samarwa da raya masana’antar Supercomputer na kasar Sin.”

Taron shekara-shekara na ISC shi ne taro mafi muhimmanci na masu ruwa da tsaki a masana’antar Supercomputer a nahiyar Turai. A shekarar 2017, ISC ya nada Lu a matsayin mamba saboda irin muhimmiyar gudummawar da ta bayar wajen samar da kwamfuta mai matukar inganci. Ita ce Basiniya ta farko kuma mace ta farko da ta zama mamban taron. A shekarar 2019 kuma aka nada ta matsayin shugabar kula da shirye-shiryen taron. Inda ta kasance mace ta farko da ta rike matsayin.

“Saboda saurin ci gaban da masana’antar Supercomputer ta kasar Sin ta samu, na samu damar samun matsayi a taron, a madadin masana kimiyya na kasar Sin. Haka kuma, yabawa ce ga kwarewata daga masana ilimi na kasa da kasa. Na yi matukar farin ciki da aka ji muryar kasar Sin a masana’antar Supercomputer ta duniya,” cewar Lu.

Lu Yutong na haskakawa a masana’atar, wanda bangare ne da maza suka mamaye fiye da mata. Mata kamar Lu, ba su da yawa a bangaren. Lu ta ce, “duk da cewa akwai mata kalilan masu bincike a wannan bangare, mata ma suna jajircewa kan aikinsu kamar maza. A hakika, mata suna da wata fa’ida ta musamman. Misali, mata masu bincike za su fi iya mayar da hankali kan bayanan fasahohin da ake son aiwatarwa da aka gabatar. Baya ga haka, hadin gwiwa tsakanin abokan aiki na da muhimmanci sosai ga manyan ayyukan injiniya na Supercomputer. Mata za su iya taka rawar gani da fa’idar da suke da ita ta mu’amala.”

Lu Yutong na fatan karin matasa za su shiga cikin binciken Supercomputer a nan gaba, domin samar da karin sauki ga mutane ta hanyar hidimomin kwamfutar samar da bayanai da saurin gaske, da taimakawa wajen kai bangaren na kasar Sin zuwa babban mataki.(Kande Gao)