logo

HAUSA

Majalisar wakilan jama'ar kasar Sin za ta bude zamanta na shekara a gobe Talata

2024-03-04 14:30:07 CMG Hausa

Majalisar wakilan jama'a ta kasar Sin (NPC), wadda ita ce majalisar dokokin kasar, ta kira taron manema labarai a yau Litinin, rana guda kafin bude zamanta na shekara-shekara.

Kakakin taro karo na 2 na majalisar NPC na 14 Lou Qinjian, ya shaidawa manema labarai cewa, zaman majalisar zai gudana ne daga gobe 5 ga wata zuwa ranar 11 ga wata. (Fa’iza Mustapha)