logo

HAUSA

Sudan na neman a mayar da matsayinta na mamba a kungiyar AU

2024-03-04 11:27:40 CMG Hausa

Shugaban gwamnatin rikon kwarya ta soji ta kasar Sudan Abdel Fattah Al-Burhan, ya nanata kwarin gwiwar da kasarsa ke da shi kan Tarayyar Afrika (AU), yana mai kira da a mayarwa kasarsa matsayinta na mamba a kungiyar.

Abdel Fattah Al-Burhan ya bayyana haka ne lokacin da ya karbi tawagar kwamitin manyan jami'an AU kan batun warware rikicin Sudan, karkashin Mohammed Ibn Chambas, a birnin Port Sudan na jihar Red Sea.

Shugaba Al-Burhan ya bayyana kwarin gwiwar da kasarsa ke da shi kan AU da kuma rawar da za ta iya takawa matukar Sudan ta zama cikakkiyar mambar kungiyar.

Ya kuma jaddada cewa, samun da mafita daga rikicin kasar ya dogara ne da janyewar dakarun RSF daga birane da kauyukan da suka mamaye.

AU dai ta dakatar da matsayin Sudan na mambarta ne tun bayan da Al-Burhan ya ayyana matakin ta baci a kasar a ranar 25 ga watan Oktoban 2021, tare da rushe majalisa da gwamnatin rikon kwarya dake karkashin Firaminista na wannan lokaci wato Abdalla Hamdok. (Fa’iza Mustapha)