Mambobin OPEC+ sun tsawaita wa’adin rage fitar da danyen mai zuwa rubu’i na biyu na shekarar bana
2024-03-04 10:16:05 CMG Hausa
Kasashe da dama mambobin kungiyar OPEC+, sun tsawaita wa’adin rage fitar da danyen mai zuwa rubu’i na biyu na shekarar nan ta bana, domin wanzar da daidaito, da ingancin kasuwannin hada-hadar cinikayyar mai.
A cewar ma’aikatar makamashi ta kasar Saudiyya, kasar dake jagorancin kungiyar OPEC, Saudiyyar ta tsawaita wa’adin rage yawan mai da take hakowa da ganga miliyan daya a kullum har zuwa karshen watan Yuni. Hakan na nufin Saudiyya za ta rika fitar da kimanin ganga miliyan 9 a kullum, har zuwa karshen rubu’i na 2 na shekarar ta bana.
A daya bangaren kuma, kasar Rasha wadda jigo ce a kawancen kungiyar ta OPEC, ita ma ta amince da rage fitar da ganga 471,000 a kullum har zuwa rubu’i na biyu na shekarar 2024, adadin da ya dan yi kasa da wanda ta rage a rubu’in farko wato ganga 500,000.
Sauran mambobin na OPEC+, ciki har da Iraki, da hadaddiyar daular Laraba, da Kuwait, da Kazakhstan, da Aljeriya da Oman, duk sun amince su tsawaita rage fitar da danyen man da suke hakowa zuwa rubu’i na biyu na bana.
To sai dai kuma wata sanarwa da OPEC din ta fitar ta nuna cewa, sannu a hankali, wannan mataki na rage fitar da danyen mai bisa radin kai, za a rika sassauta shi gwargwadon yanayin kasuwannin mai, ta yadda hakan zai karfafi daidaiton kasuwannin man bayan watan Yuni.(Saminu Alhassan)