logo

HAUSA

An bude taron shekara-shekara na majalisar bada shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin

2024-03-04 15:53:58 CMG Hausa

An bude zama na biyu na taron majalisar bada shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin wato CPPCC, da wajen karfe 3 na yammacin yau Litinin a birnin Beijing, inda shugaban majalisar Wang Huning ya gabatar da rahoton aiki a madadin zaunannen kwamitin majalisar ta CPPCC. Rahoton da ya gabatar dai ya waiwayi ayyukan da majalisar ta gudanar a shekara daya da ta gabata, kana ya gabatar da shirin gudanar da ayyukan shekarar bana.

A yayin taron majalisar CPPCC na kwanaki 6, membobin majalisar fiye da dubu biyu, wadanda suka zo daga bangarori 34 za su saurari, tare da dudduba, da kuma tattauna kan rahoton aikin zaunannen kwamitin majalisar ta CPPCC, da rahoton daftarin ayyuka da aka gabatar, kana za su halarci taron shekara-shekara na majalisar wakilan jama’ar kasar Sin, inda za su saurari, da tattauna rahoton aikin gwamnatin kasar, da bada shawara a fannonin siyasa, da tattalin arziki, da zaman rayuwar jama’a da sauransu.

Majalisar ba da shawarwari kan harkokin siyasar kasar Sin wato CPPCC, tsari ne dake nuna salon musamman na kasar Sin, kana, muhimmiyar hukuma ce ta hadin-gwiwar jam’iyyu daban-daban gami da gudanar da shawarwarin siyasa a karkashin jagorancin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin, kuma, muhimmiyar hanya ce da ake bi wajen aiwatar da demokuradiyya daga dukkanin matakai a cikin harkokin siyasar kasar, kuma muhimmin bangare ne a cikin tsarin mulkin kasar.

Kwamiti na membobin kasa baki daya na CPPCC, kungiya ce dake aiwatar da tsarin CPPCC, wanda ke kunshe da wakilai daga jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin, da sauran jam’iyyun demokuradiyya da ba na kwaminis ba, da wadanda ba sa cikin kowace jam’iyya, da rukunonin al’umma, da wakilai daga kananan kabilu da bangarori daban-daban, da wakilan ‘yan uwanmu daga Taiwan da Hong Kong da Macau, da wakilan Sinawa mazauna kasashen waje da suka dawo da dai sauran wasu bakin da aka ba su goron gayyata na musamman. Manyan ayyukansu su ne, gudanar da shawarwari kan harkokin siyasa, da sa ido bisa tafarkin demokuradiyya, da kuma halartar harkokin siyasa da ba da shawarwari. Wadannan muhimman ayyukan uku sun nuna yadda ‘yan jam’iyyun siyasa gami da kungiyoyi daban-daban, da mutane daga kabilu da bangarori daban-daban suke shiga cikin harkokin kasa, gami da taka muhimmiyar rawarsu a cikin tsarin siyasar kasar Sin, kana, muhimmiyar alama ce dake bambanta majalisar CPPCC da sauran kungiyoyin siyasa.

Shekaru biyar ne wa’adin aikin kowane zagayen ‘yan majalisar CPPCC, kuma a kan gudanar da cikakken zamanta sau daya a kowace shekara. (Zainab Zhang/Murtala Zhang)