logo

HAUSA

Shugaban Aljeriya ya bayyana niyyar karfafa huldar kasarsa da kasar Iran

2024-03-04 14:38:13 CMG Hausa

Shugaban kasar Aljeriya Abdelmadjid Tebboune ya bayyana a jiya Lahadi, a birnin Algiers na kasarsa, cewa yana son ci gaba da inganta hulda tsakanin kasashen Aljeriya da Iran.

Haka kuma a jiyan, kasashen 2 sun daddale dimbin yarjejeniyoyin hadin gwiwa masu alaka da makamashi, da sabbin kamfanoni, da yawon shakatawa, da watsa labarai, da wasannin motsa jiki, da dai sauransu.

A wajen taron manema labaru da shugaba Tebboune ya kira, tare da takwaransa na kasar Iran Seyed Raisi, bayan bikin kulla yarjejeniyoyi a tsakanin kasashensu biyu, shugaban na kasar Aljeriya ya ce, tushen huldar kasashen 2 shi ne kauna da kokarin hadin kai, kana ya yi alkawarin kara kyautata wannan hulda zuwa wani sabon matsayi. Ban da haka, shugaba Tebboune ya bayyana gamsuwa kan yadda shugaban kasar Iran ke kokarin rufawa Falasdinawa baya.

A nasa bangare, shugaba Raisi na kasar Iran ya ce huldar dake tsakanin kasarsa da Aljeriya na da zurfi, kana ya jaddada bukatar dogaro kan matasa a kokarin habaka hadin kan kasashen 2 ta fuskar tattalin arziki.

(Bello Wang)