Yan sama jannatin Sin sun kammala aikin gyara na’ura a wajen kumbo a karon farko
2024-03-02 15:44:52 CMG Hausa
Ofishin kula da ayyukan kumbon da ke daukar 'yan sama jannati na kasar Sin, ya ba da labarin cewa, da misalin karfe 1 da mintuna 32 na yammacin ranar Asabar din nan, ‘yan sama jannatin kumbon Shenzhou-17, wato Tang Hongbo, da Tang Shengjie, da Jiang Xinlin, sun yi nasarar kammala aikin da aka tsara a wajen kumbon su, cikin tsawon kusan sa’o’i 8, bisa tallafin na’urori da masanan kimiyya da fasaha dake doron duniya ke sarrafawa.
Kawo yanzu, Tang Hongbo, da Jiang Xinlin, sun riga sun koma sassan dakin gwaje-gwaje na Wentian. Wannan ne karo na biyu da tawagar ‘yan sama jannatin kumbon Shenzhou-17 na kasar Sin, ta yi nasarar gudanar da aiki a wajen kumbon.
Kaza lika, wannan ne karo na farko da ‘yan sama jannatin kasar Sin suka kammala aikin gyara na’urar samar da wutar lantarki, ta sashen Tianhe a wajen kumbon.
Bisa shirin da aka tsara, ‘yan sama jannatin kumbon Shenzhou-17 na kasar Sin, za su gudanar da jerin gwaje-gwajen kimiyya da fasaha da dama a sararin samaniya. (Jamila)