logo

HAUSA

Nijar-Benin: Bayan janye takunkumin CEDEAO, Nijar ta rike rufe iyakarta da Benin

2024-03-02 15:46:34 CGTN HAUSA

 

Takunkumin CEDEAO kan Nijar an janye shi a ranar Asabar din da ta gabata, bayan wani taron gaggawa na kungiyar a birnin Abujan Najeriya. Takunkumin da aka dauka bayan juyin mulkin ranar 26 ga watan Yulin shekarar 2023. Watanni fiye da 6, iyakoki tsakanin Nijar da Benin sun kasance rufe. A yanzu, hukumomin Cotonou sun bude iyaka, yayin da a bangaren Nijar take rufe.

Daga birnin Yamai, abokin aikinmu ya duba wannan al’amari ga kuma rahoton da ya hada mana.