Putin ya zargi kasashen yammacin duniya saboda kutsa kai da suka yi cikin harkokin gidan Rasha
2024-03-01 13:00:13 CMG Hausa
Shugaban kasar Rasha, Vladimir Putin ya zargi kasashen yammacin duniya a jiya Alhamis 29 ga watan Fabrairu, saboda yunkurin da suke yi na tsoma baki cikin harkokin gidan kasarsa, inda ya kuma jaddada cewa, Rasha za ta zabi turbar da ta dace da ita na samun ci gaba.
Yayin da yake gabatar da jawabin shekara-shekara ga majalisun dattawa da wakilan kasar, Putin ya ce kasarsa ba za ta yarda da shisshigin da wasu mutane ko kasashe suke yi mata ba, kuma kasashen yammacin duniya na son raunata karfin Rasha ta hanyar ta da rikici, amma ba za su ci nasara ba. Putin ya kara da cewa, al’ummar kasarsa za su kare hakkinsu na rayuwa cikin lumana, da ’yancinsu na zabar hanyar samun ci gaba.
Har wa yau, Putin ya ce, Rasha na fatan gudanar da shawarwari tare da Amurka, dangane da batun tabbatar da zaman karko bisa manyan tsare-tsare, amma ba zai yiwu a gudanar da shawarwarin ba, in ba tare da la’akari da batun tsaron Rasha ba.
Shugaba Putin ya yi kashedin cewa, duk wani sabon shisshigin da za’a yi wa harkokin cikin gidan Rasha, zai iya haifar da babban rikicin da zai kai ga amfani da makaman nukiliya. (Murtala Zhang)