logo

HAUSA

Falasdinawa 112 sun mutu a Gaza sanadiyyar wani harin Isra’ila kan masu neman agaji

2024-03-01 10:21:12 CMG Hausa

 

Majiyoyin ma’aikatan tsaro da jinya a Falasdinu sun ruwaito cewa, akalla Falasdinawa 112 sun mutu yayin da wasu 760 suka jikkata, sanadiyyar wani harin da Isra’ila ta kai kan fararen hula dake jiran karbar agaji a yankin yammacin birnin Gaza.

A martaninta game da aukuwar lamarin, kungiyar Hamas ta yi barazanar dakatar da yarjejeniyar tsagaita bude wuta da Isra’ila. Yayin da fadar shugaban Falasdinu ta yi tir da harin, tana mai cewa, wani bangare ne na yakin kisan kiyashi da Isra’ila ta kaddamar kan al’ummar Falasdinu.

Kakakin MDD ya ruwaito a jiya cewa, shi ma sakatare janar na majalisar Antonio Guterres, ya yi tir da harin da ya yi sanadin kisan Falasdinawa sama da 100, wadanda ke jiran agaji a arewacin Gaza.

Har ila yau, Antonio Guterres ya nanata kiran dakatar da bude wuta nan take tare da sakin mutanen da aka yi garkuwa da su ba tare da gindaya sharadi ba. Ya kara da kira da a dauki matakai na gaggawa ta yadda muhimman kayayyakin agaji za su samu damar shiga yankin Gaza ga mutane mabukata. (Fa’iza Mustapha)