Xi Ya Jaddada Bukatar Raya Sabon Makamashi Mai Inganci A Kasar Sin
2024-03-01 14:26:43 CMG Hausa
Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya jaddada bukatar inganta raya sabon makamashi a kasar, domin bayar da karin gudummuwa ga gina duniya mai tsafta da aminci.
Xi Jinping wanda shi ne sakatare janar na kwamitin kolin JKS, ya bayyana haka ne a jiya, yayin wani zaman nazari na ofishin kula da harkokin siyasa na kwamitin kolin.
Da yake bayyana wadatawar makamashi a matsayin wanda ke da tasiri kan baki dayan sassan tattalin arziki da rayuwar al’umma, ya ce raya makamashi mai tsafta da inganta kare muhalli da rage sinadarin Carbon, wata matsaya ce da kasashen duniya suka cimma dangane da tunkarar matsalar sauyin yanayi.
Ya kuma jaddada bukatar hada aikin raya sabon makamashi da na wadatar makamashi a kasar da mayar da hankali kan muhimman fasahohi da gina ingantaccen tsarin kayayyakin samar da makamashi mai tsafta da zurfafa hadin gwiwa da kasa da kasa, tare da kai wa matsayin dogaro da kai a bangaren makamashi da na raya fasahohi. (Fa’iza Mustapha)