logo

HAUSA

Sojojin Nijeriya sun kashe wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne 974 a watan Fabrairu

2024-03-01 10:06:00 CMG Hausa

 

Rundunar sojin Nijeriya ta sanar da cewa, dakarunta sun kashe wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne da yawansu ya kai 974, yayin mabambantan ayyukan da suka aiwatar cikin watan Fabrairu, a fadin kasar mafi yawan al’umma a nahiyar Afrika.

Kakakin rundunar sojin Edward Buba, ya shaidawa manema labarai jiya Alhamis a Abuja, babban birnin kasar cewa, baya ga wadanda aka kashe, an kuma cafke wasu da yawansu ya kai 621.

Edward Buba ya kara da cewa, sojojin sun kuma ceto akalla mutane 466 da aka sace, tare da kwato makamai iri daban daban guda 1,573 da albarusai 23,345, duk a cikin watan na Fabrairu.

Ya ce, a yankin arewa maso gabashin kasar kadai, an kashe jimilar ‘yan ta’adda 242, ciki har da manyan kwamandoji 3 na kungiyar IS a yankin yammacin Afrika. (Fa’iza Mustapha)