logo

HAUSA

Sassan ma’aikatun gwamnatin kasar Sin sun gudanar da shawarwari 12,480 a shekarar 2023

2024-03-01 10:47:24 CMG Hausa

Sassan ma’aikatun gwamnati dake karkashin majalisar gudanarwar kasar Sin sun gudanar da shawarwari da tsare-tsare 12,480 da wakilan majalisar wakilan jama’ar kasar Sin da mambobin kwaminitin majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin suka gabatar a shekarar 2023, kamar yadda kakakin ofishin yada labarai na majalisar gudanarwar kasar Sin ta bayyana a ranar Alhamis. 

Sassan sun yi amfani da shawarwari 7,955, wanda ya kai kashi 95.7 cikin dari na dukkan shawarwarin da aka gabatar, da tsare-tsare 4,525 wato kashi 96.5 cikin dari na dukkan tsare-tsare da aka gabatar, a cewar kakakin, Xing Huina a taron manema labarai.

Xing ta bayyana cewa, sassan sun fitar da matakai sama da 2,000 bisa wasu shawarwari da tsare-tsare guda 4,700 a shekarar da ta gabata, tare da samun ci gaba wajen inganta ci gaban tattalin arziki da tabbatar da kyautatuwar rayuwar jama'a. (Muhammed Yahaya)