logo

HAUSA

A bara adadin dalibai Sinawa dake karatu a manyan makarantu ya kai sama da miliyan 47

2024-03-01 21:11:50 CMG Hausa

Alkaluma daga ma’aikatar ilimi ta kasar Sin sun nuna a shekarar 2023 da ta gabata, adadin dalibai Sinawa dake karatu a manyan makarantun gaba da sakandare sun haura miliyan 47.63, adadin da ya karu da miliyan 1.08 kan na shekarar da ta gabace ta, ko karin kaso 2.32 bisa dari a shekara.

Alkaluman da ma’aikatar ilimi ta Sin ta fitar a Juma’ar nan, sun nuna yadda kasar ta samu bunkasar adadin manyan makarantu zuwa 3,074 a shekarar ta bara, adadin da ya karu da kaso 61 bisa dari kan na shekarar 2022.

Kaza lika a dai 2023n, adadin malamai masu yin cikakken aikin koyarwa a manyan makarantun sassan kasar ya kai miliyan 2.07, adadin da ya karu da kaso 4.91 bisa dari kan na shekarar da ta gabace ta.  (Saminu Alhassan)