logo

HAUSA

Yadda Sin Ke Dora Muhimmanci Ga Zamanintarwa Da Ci Gaba Mai Inganci

2024-02-29 17:39:36 CGTN HAUSA

DAGA SAMINU ALHASSAN

Kasar Sin ta wuce gaba wajen kafa kyakkyawan misali na samar da ci gaba, ta kuma zama abun koyi ga sauran kasashen duniya a fannin gaggauta bunkasuwa. Salonta na ci gaba cikin lumana, ya kai ga nasara ne sakamakon albarkatu, da manufofin da take da su masu dacewa da ainihin halin da kasar ke ciki.

Tabbas al’ummar kasar Sin na da kwazo aiki, kuma mahukuntan kasar na tsara manufofi managarta dake share fagen karfafa gwiwar jama’arta, ta yadda suke iya cimma cikakkiyar nasarar raya kasarsu tare. Irin saurin ci gaba da Sin ta cimma cikin shekaru 45 na baya bayan nan sun baiwa kowa mamaki, inda ta zama zakaran gwajin dafi a tarihin rayuwar bil adama.

Kasar Sin ta yi fice a dukkanin fannonin samar da ci gaba, ciki har da raya ilimi, kimiyya da fasaha, noma, raya masana’antu, bunkasa tattalin arziki, da daga martabar zamantakewa walwalar al’umma.

Ana hasashen a yayin manyan taruka biyu na Sin na shekarar nan ta 2024, wato taron shekara-shekara na majalisar wakilan jama’ar kasar, da na majalisar ba da shawarwari kan harkokin siyasa ta kasar, za a kara tattaunawa wadannan muhimman sassa, wato zamanintar da kasa da bunkasa ci gaba mai inganci.

A wannan gaba da Sin ke kara bude kofofinta ga duniya, sassan kasa da kasa na kara fahimtar hanyar zamanintarwa ta Sin, salon gurguzu mai halayyar musamman ta Sin dake gudana karkashin jagorancin JKS.

Kasar Sin ta nunawa duniya misali na hadakar aiki tukuru da kyakkyawan jagoranci, wanda ke haifar da ci gaba ga al’umma mafi yawa a duniya, al’ummar dake cin gajiyar walwala da wadata, wadda kuma ta yi fice a fannonin raya al’adunta na fil azal, mai kyautata dangantaka tsakanin rayuwar bil adama da halittun dake kewaye da shi cikin lumana, kana al’ummar dake ci gaba da samun bunkasuwa cikin kwanciyar hankali.