logo

HAUSA

Xi ya jaddada ba da gudummawa ga zamanantar da kasar Sin da ayyuka masu inganci

2024-02-29 11:26:14 CMG Hausa

Shugaba Xi Jinping ya yi kira ga jami’ai a dukkan matakai da su rungumi irin tsarin koyo na Markisanci wajen hada bayani da aiki, ta yadda za su ba da gudummawa wajen ciyar da zamanantar da kasar Sin gaba da ayyuka masu inganci.

Xi, wanda kuma shi ne babban sakataren kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin, kana shugaban kwamitin koli na soja, ya bayyana hakan ne a cikin gabatarwar da ya rubuta a cikin kasidar bayani na rukuni na shida na jami’an da ke daukar horo. (Yahaya)