Sin ta lashe kofin gasar kwallon tebur ta mata karo na 6 a jere
2024-02-29 14:28:31 CGTN HAUSA
Kungiyar kwallon tebur ta mata ta kasar Sin, ta yi nasarar lashe kambin gasar kasa da kasa, wadda hukumar ITTF ke shiryawa, bayan da ta yi nasarar doke takwararta ta kasar Japan da ci 3 da 2, a wasan karshe da aka buga a karshen mako. Da wannan nasara, yanzu haka Sin din ta lashe wannan gasa sau 6 ke nan a jere. Kaza lika da nasarar ta wannan karo, Sin din ta lashe wannan kofi na Corbillon sau 23 a tarihi.
Tawagar ‘yan wasan kwallon tebur ta Sin mai kunshe da Sun Yingsha, da Chen Meng da Wang Yidi, sun jagoranci nasarorin da Sin ta samu a wannan babbar gasa har sau 5 a jere, tun daga shekarar 2014.
Sun ta buga wasa da abokiyar karawarta mai shekaru 15 a duniya Miwa Harimoto a wasan bude gasar. ‘Yan wasan 2 sun kammala zagayen farko na karawar Sun na da maki 3 Miwa na nema, daga karshe Sun ta yi gaba da jimillar maki 11, ita kuma Miwa na da 5 a wasan na farko.
A wasa na biyu kuwa an fafata sosai, inda Harimoto ta yunkuro zuwa kunnen doki da maki 8, kafin daga bisani Sun ta samu maki 3 a jere, ta kuma kai ga lashe duka wasannin biyu da suka kara.
Dukkanin sassan biyu sun ci gaba da fafatawa, inda ‘yar wasan ta daya a duniya wato Sun, ta yi gaba da maki 4 da 1 a zagaye na 3 na wasan, wanda hakan ya tursasa Harimoto kaiwa makurar karshen lokaci ba tare da samun nasara ba. Daga karshe Sun ta lashe wasan da maki 11 da 4, wanda ya tabbatarwa tawagar kasar Sin da nasarar da take nema.
A nata bangare kuwa, Chen Meng ta yi nasara a duk wasanni 7 da ta buga da takwararta ta Japan Hina Hayata. A wannan karo ma Chen Meng wadda ke rike da lambar zinari ta gasar Olympic, ta mamaye wasan farko, inda suka tashi wasan tana da maki 11 Hina kuma na da maki 6.
A wasa na 2 kuwa, Hayata ta dage kwarai inda suka tashi da maki 10 da 6, da kuma maki 11 da 8. Daga nan sai Hayata ta canza salo, ta lashe wasa na gaba da ci 10 da 5, ta kuma kaucewa turjiyar Chen inda a wasa na 3 suka tashi maki 11 da 9.
A wasa na 4 kuwa, Chen ta yi nasarar wucewa gaba tun da wuri, kafin Hayata ta mayar da wasan kunnen doki mai maki 7. Duk da cewa Chen ta samu maki 5 a jere, Hayata ta yi kokari matuka har ta kai ga sun kammala wasan da ci 14 da 12.
Miu Hirano ta Japan, ta samu nasara a wasannin da ta kara da Wang Yidi mai rike da kambin duniya a matsayi na 2, inda suka fafata, da kammala wasannin su da maki 11 da 8, da 13 da 11, da kuma 12 da 10, wato wasa daya ya rage Japan din ta samu nasarar lashe zagayen.
A wannan lokaci ne kuma Sun ta sake yunkurowa, a fafatawar ta da Hayata, inda jimillar makin su ya kai ga 11 da 2, da 11 da 7, da kuma 11da 6, kuma da wannan nasara ne tawagar ta Sin ta shige gaban ta Japan.
A kuma wasan Chen na gaba, ‘yar wasan ta Sin ta farfado daga rashin nasarar ta da ci 3 da 1 a wasan farko da suka fafata da Harimoto, wadda ke rike da matsayi na 16 a duniya. Da kuma wannan karawa ne gasar ta kawo karshe, bayan shafe sa’o’i sama da 3 da rabi ana fafatawa.
Bayan Harimoto ta wuce gaba da maki 11 da 4, sai Chen ta mayar da martani da maki 11 da 7 a wasan su na 2. Kuma la’akari da muhimmancin wasa na 3, ‘yan wasan 2 sun zage damtse, inda suka yi kunnen doki da maki 8, kafin daga bisani Chen ta wuce gaba da maki 3 a jere. Dakin wasa na “Busan” ya barke da Shewa lokacin da Chen ta lashe makin karshe na wasan na 4, inda suka tashi ci 11 da 7.
A bangaren wadanda suka lashe lambobin tagulla a gasar ta kwallon tebur kuwa, akwai tawagar Faransa, da Hong Kong, da Sin.
Kafin hakan ma tawagogin kasashen Sin, da Faransa ajin maza, sun kai ga zagayen wasan kuda da na karshe, bayan da Sin ta doke koriya ta kudu, yayin da ita kuma Faransa ta doke yankin Taipei da ci 3 da 1.
A ajin na maza, Fan Zhendong daga Sin ya yi rawar gani, inda ya dakile rashin nasarar da tawagar Sin ta kusa gamuwa da ita, yayin da Wang Chuqin ya ci wasan sa na biyu, bayan da ya yi rashin nasara a wasan farko na bude gasar.
A bangaren tawagar kasar Faransa kuwa, dan wasan ta dake rike da matsayin kwarewa na 6 a duniya Felix Lebrun, ya nuna bajimta kwarai, inda ya lashe wasanni biyu, kuma da hakan ya kai Faransa zuwa wasan karshe na gasar a karon farko tun bayan shekarar 1997.